Monday, 9 September 2019

Kalli jirgin ruwan me kungiyar Chelsea, Roman Abramovic na Naira biliyan 181

Me kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovic dan kasar Rasha wanda hamshakin attajirine da ke da kudin da suka kai dala biliyan 12.5 kwatankwacin Naira triliyan 4.5 kenan ya sayi daya daga cikin jiragen ruwa na shakatawa mafiya girma a Duniya.Sunan jirgin ruwan Eclipse wanda ya siya akan dala miliyan 500 kwatankwacin Naira biliyan 181 kenan.


Wani kamfanin kasar jamus ne ya kerawa Abramovic wannan jirgin ruwa me girman kafa 533 hakan na nufin jirgin ya nunka filin buga kwallon Chelsea sau 2. An kwashe shekaru 5 ana kera jirgin, bayan gwaje-gwaje da kammala kerashi a shekarar 2009, an mikawa Abramovic jirgin a shekarar 2010.


Akwai kudiddifin ninqaya 2 a cikin jirgin kuma shine jirgin ruwan mutum daya me kudiddifin ninqaya mafi girma a Duniya, akwai asibiti, da gidan con abinci, da gurin gyaran kai da gidan rawa, da cinima dadai sauransu.


Jirgin nada jiragen sama masu saukar Angulu guda biyu da gurin saukarsu da kuma kananan jiragen ruwa da kuma kananan jiragen ruwa masu tafiya a karkashin ruwa.


Jirgin ruwan nada na'urorin dake gano makaman da aka harbo kuma gilasan cikinshi harsasai basa hudashi hakanan gilasan cikin jirgin ba zasu bari kaga na ciki ba.


Jirgin nada ma'aikata 70 sannan sannan zai iya daukar baki 37 a lokaci guda, ana kashe Yuro miliyan 30 kusan Naira Biliyan 12.2 duk shekara wajan kula da jirgin.
A shekarar 2010 jirgin na Abramovic shine jirgin ruwa mafi tsada da girma a Duniya kamin shugaban Abu Dahbi, Khalifa bin Zayed al-Nayan ya sai nashi na kusan fan miliyan 500.

A yanzu jirgin ruwan na Abramovic shine na 4 mafi girma a Duniya.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment