Sunday, 15 September 2019

Kalli matar marigayi Mugabe na wa Obasanjo kuka

A jiyane aka yi jana'izar marigayi tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe a Harare babban birnin kasar inda shuwagabannin kasashe daban-daban suka halarta.
Daga Najeriya mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya wakilci gwamnati sannan akwai kuma tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da shima ya halarci jana'izar.

A wannan hoton na sama matar tsohon shugaban kasarce, Grace Mugabe take kuka a gaban Obasanjo.
A wajan jana'izarne dai akaiwa shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ihun da nuna ba'ason jin jawabinshi bayan harin kyamar baki da 'yan kasarshi suka rika kaiwa sauran 'yan kasashen Afrika.

Mugabe ya mutu yana da shekaru 95 bayan daya shafe kusan shekaru 40 yana mulkar Zimbabwe.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment