Sunday, 8 September 2019

Kalli Pogba da budurwarshi da dansu suna shakatawa


Man.U star Paul Pogba and girlfriend Maria Salaues take their son for a sunny stroll in Saint Tropez (Photos)
Tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa me bugawa Manchester United wasa, Paul Pogba kenan a wadannan hotunan yayin da yake shakatawa da budurwarshi, Maria Zulay Salaues da dansu a birnin Saint Tropez na kasar Faransa.

Pogba be samu bugawa kasarshi Faransa wasan neman buga kofin Europa ba da suka yi da kasar Albania saboda raunin da yake dashi dan haka yayi amfani da wannan lokacin hutu dan zuwa yawon shakatawa da iyalanshi.

A watan Janairu na wannan shekararne Pogba da budurwar tashi suka samu karuwar da na miji.

A watan Mayun daya gabatane dai budurwar ta Pogba ta yi wani abu dake nuna kamar sunyi aure ita da masoyin nata inda ta canja sunanta suwa Zulay Pogba a shafinta na Instagram sannan kuma ta saka wani hotonsu tare inda ta rubuta cewa"har abada"

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment