Monday, 23 September 2019

Kalli yanda aka kama wata iyamura dake makantar karya tana bara

An kama wata mata Inyamura me suna Nzube Ekene tare da wata yarinya 'yar shekaru 10 da ta yi safarar ta take amfani da ita tana bara a matsayin makauniyar karya.
An kama matarne me 'ya'ya 2 a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti bayan da asirinta ya tonu.


Asirin matar ya tonune ta hannun shugabar kungiyar mata lauyoyi, FIDA reshen jihar ta Ekiti, Mrs Seyi Ojo inda ta zo wucewa tace sai ta ga yarinyar tazo tana mata bara, bayan data koma ofis sai ta sa aka kora mata matar dan ta taimaka musu, tace amma sai aka gano ashe makantar karyace.

Ta kara da cewa matar na sanye da kaya masu kyau a cikin jikinta amma a zahiri ta saka yagaggun kaya ta kuma saka hular malafa dan a tausaya mata.

Yarinyar me suna Ada ta ti farin ciki sosai da aka kubutota daga hannun matar inda ta rungume shugabar lauyoyin tana murna.

Ada ta bayyana cewa Ekene ta je gurin mahaifiyarta inda ta nemi ta bata ita suje ta tayata kasuwanci, ta kuma yi alkawarin sakata makaranta amma da suka zo sai ta sata tana bara a maddinta, tace ta roketa ba zata iya ba amma ta dake ta ta sata dole.

Ada ta kara da cewa Ekene ta hanata ganawa da mahaifiyarta inda ta yaga littafin data rubuta lambar mahaifiyartata.

A lokacin da aka kama Ekene misalin karfe 11 na safe an same ta kudi kimanin Naira dubu 11 ta kuma amsa cewa ta wa mahaifiyar Ada karyar cewa Kasuwanci ta ke yi, ta kara da cewa rashin aikin yi ne ya jefata wannan hali.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment