Sunday, 15 September 2019

Kalli yanda dan shekaru 32 yayi ikirarin zama dan shekaru 82 dan ya shiga kasar Amurka

Wannan wani mutum ne dan kasar India me suna, Jayesh Patel dan shekaru 32 da yayi shigar tsaffi ya kuma yi ikirarin zama dan shekaru 82 dan dai ya samu shiga kasar Amurka.Asirinshi ya tonu a yayin da yaje filin jirgin sama yana shirin bain India, ya wuce shingen jami'an tsaro na farko, saidai a na biyune yayin da yake shirin mai bincike sai yace bazai iya tsayuwa ba.

Saidai kuma daga baya an lura cewa yana kakkauda kai baya son hada ido da jami'an tsaron, wannan yasa aka fara bincikarsa. Da bincike yayi nisa sai aka ga shekarunshi 82 a fasfonshi amma a zahiri kamar ba gaskiya bane.

A haka dai asirinshi ya tonu aka kuma mikashi gurin jami'an tsaro.

Ya shiryane da wani ajan inda ya mai shigar tsaffi da niyyar idan yayi nasarar zuwa kasar Amurka zai biyashi kudin aiki.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment