Wednesday, 18 September 2019

Kalli yanda dan wasan baya na Napoli, Kalidou ya zama dutse ya hana Liverpool sakat a wasan jiya

A wasan jiya, tsakanin Liverpool da Napoli tauraron dan wasan baya da akewq kallon shine na daya a Duniya a yanzu, Virgil Van Dijk ya kwafsawa Liverpool inda ya bayar da kwallon da aka cita ta biyu, wannan yasa da yawa suka rika mai ba'a a shafukan sada zumunta. A bangare guda kuma dan wasan baya na Napoli, Kalidou Koulibaly wanda shima gwanine a wajan tare yayi kokari sosai a wasan na jiya.
Dan kasar Senegal na daya daga cikin 'yan wasan baya da akewa kallon sun iya aikinsu a nahiyar turai. A wasan jiya ya zama kamar dutse a bayan Napoli inda ya hana 'yan ukun Liverpool, Salah, Mane da Firmino da akewa kallon gwanayen cin kwallo a Duniya sakat.

Wani hoton Kalidou da ya kaiwa Salah karo da kai ya dauki hankula sosai inda yayi hakan wajan ganin ya tare Salah din amma a zahiri Salah ya wuce da kwallon.

A wasan na jiya dai Liverpool bata kai hari ko guda daya me kyau ba

Wannan yasa wasu ma'abota shafin Twitter suka rika hada Kaludou da Van Dijk.

Saidai shima fa Kalidou a wasan da suka buga da Juventus a watan Augusta daya gabata ya ci kungiyar tashi ta Napoli kwallo bisa kuskure, dan haka Shim Van Dijk kuskurene wanda kowa na iya yi.

Kalidou ma gwanine dan sau 3 yana fuskantar 'yan 3 na Liverpool a gasar Champions League amma kwallo daya suka taba cinshi. Bajintar da ya nuna jiya tasa wani me sharhi a BT Sports ya ke baiwa Manchestee City shawarar ta saye ahi tunda yanzu tana da matsalar dan wasan baya.

Manchester United ta nemi kalidou a kasuwar saye da sayarwar 'yan wasan da aka bude data gabata inda ta tayashi akan Fan miliyan 100 amma Napoli tace mata albarka.

Kalli hotunan taren da Kalidou ya wa Napoli jiya da bidiyon karon daya kaiwa Salah da kai.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment