Friday, 13 September 2019

Kalli yanda Mansura Isa ta fashe da kuka saboda takaicin halin da ilimin 'ya'yan talakawa ke ciki

Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa kuma mata a gurin tauraron fina-finan Hausa, Sani Musa Danja, Zaki, Watau Mansurah Isah wadda a yanzu ta shahara wajan bayar da taimako ga marasa galihu ta zubar da hawaye akan yanda halin da ilimin 'ya'yan talakawa yake ciki.A wani bidiyon ta daya watsu sosai a shafukan sada zumunta anga Mansurah tana caccakar shuwagabanni da masu kudi kan yanayin ilimin da 'ya'yan talakawa ke ciki inda ta tambayi shin wai kudin da akewarewa ma'aikatar ilimi duk shekara daga kasafin kudi, me ake yi dasu?

Mansurah ta bayar da labarin yanda suka je wata makaranta me aji daya tal ta tambayi malaman shin wai idan ana ruwa ya suke yi da yaran?

Ya bata amsar cewa a aji daya suke tarasu.

Mansurah ta fashe da kuka cikin sheshekar kuka tana kira ga shuwagabanni da masu kudi su gyara.

Kalli cikakken bidiyon a kasa:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment