Monday, 16 September 2019

Kalli Yanda Ronaldo ya fashe da kuka saboda mahaifinshi be shaida nasarorin daya samu ba

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya fashe da kuka saboda kewar mahaifinshi a yayin da shahararren dan jaridarnan na kasar Ingila, Piers Morgan ke hira dashi.


Ronaldo ya bayyana cewa be san mahaifinshi, Danis daya mutu a shekarar 2005 sosai ba saboda mashayin giyane basa wata hira irin ta da da uba a koda yaushe yana kyararshine.

Da aka saka mai hirar mahaifin nashi da aka taba nada kamin ya mutu, Ronaldo ya fashe da kuka inda yace bakin cikinshi shine gashi yana ta samun karramawa a Duniya a matsayin tauraron dan kwallo amma mahaifin nashi be shaida hakan ba.
Ronaldo kenan a wannan hoton tare da Mahaifiyarshi,Dolorez da marigayi mahaifinshi, Daniz wanda tsohon sojane.

Da yake magana akan budurwarshi, Georgina Rodriguez, Ronaldo yace uwar 'ya'yanshi ce kuma yana sonta, ta bude mai zuciyarta shima ya bude mata tashi, kamar yanda The Sun UK ta ruwaito.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment