Sunday, 8 September 2019

Kalli yanda Ronaldo ya kullewa 'yan kasar Serbia baki dake mai ihun Messi! Messi!!

Tauraron dan kwallon kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya rufewa magoya bayan kasar Serbia baki a wasan da Portugal din ta je gidan Serbia suka buga na neman zuwa gasar Euro 2020.
A lokacin da ake buga wasan jiya Asabar duk lokacin da Ronaldo ya dauki kwallo, magiya bayan Serbia sukan rinka kiran sunan Messi Messi dan su daburtashi.

Saidai a tarihin Ronaldo, irin wannan abin baya sa ya rikice ko kuma yayi fushi zama a iya cewa hakan yakan zaburar dashine dan ganin ya ba masu mai ihun kunya.

Haka kuwa aka yo, ana mintina 80 da wasa Ronaldo ya ciwa Portugal kwallo ta 3 inda ya rufewa magoya bayan Serbian baki daga ihub da suke mai.

Serbin ta rama kwallonta ana minti 85 da wasa ta hannun Mitrovic Saidai Bernardo Silva ya ciwa Portugal kwallo ta 4 inda aka tashi wasan 4-2Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment