Monday, 16 September 2019

Kalli yanda Wani bawan Allah ya mayar da wasu yara masu talla makaranta

Wannan bawan Allahn wani dan siyasane me suna Sulaiman Ibrahim Dabo dake garin Zaria na jihar Kaduna, ya bayyana cewa ya hadu da wadannan kananan yara da aka ganshi a hotunan nan tare dashi a Kofar Doka, Zaria suna tallar Mazarkwaila/Suga Rawan Doki, saboda yaga yarane sosai ya tsaya yake musu tambayoyi.
Yace ya tambayesu sunan unguwarsu da sunayensu dana iyayensu, sun gaya mai Yarinyar sunanta A'isha shi kuma yaron sunanshi Isah sun kuma gayamai sunan unguwarsu amma sun kasa mai kwatancen gidansu. Yace a karshe dai ya tambayesu nawane abinda suke sayarwa gaba dayanshi? Suka ce mai dubu biyu da dari biyar, yace kadan ya rage ya zubar da hawaye, nan ya dauki dubu 3 ya basu.

Sai ya kira wani abokinshi dake unguwar da suka ce, ya tura mai hotunansu dan ya binciki inda suke, ya kara da cewa abokin nashi a karshe ya gano gidan yaran sannan ya baiwa mahaifinsu lambar wayarshi suka yi magana.

Yakara da cewa ya gayawa mahaifin illar tallar da yaran suke kuma ya tambayeshi dalilin fitar dasu daga makaranta sai yace mai ya shiga matsalar rashin kudine shiyasa, Sulaiman ya kara da cewa, ya nemi izinin uban kan saka yaran makaranta kuma ya mince mai.

Yanzu dai ya sakasu wata sabuwar makaranta me suna ZEDA inda yace yana fatan Allah ya Albarkaci rayuwarsu.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment