Saturday, 14 September 2019

Kalli yanda wata mata da karamar diyarta ta tare a ofishin jakadancin najeriya dake Afrika ta kudu tana jira a dawo da ita gida

Wannan hoton wata matace 'yar Najeriya tare da karamar diyarta da ta koma bakin ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Afrika ta kudu ta tare da zama dan jiran zagaye na biyu na kwasho 'yan Najeriya zuwa gida da akeyi sana diyyar fadan kyamar baki daya ritsa dasu acan.Matar ta fayawa manema labarai cewa kusan shekararta 5 da zuwa kasar ta Afrika ta kudu amma wadannan hare-hare sun sa an kona shaguna ciki hadda dakin da take Zaune dan haka gara ta koma gida.

Tace zata ci gaba da zama a wajan har zuwa randa za'a sake zuwa kwashe 'yan Najeriyar dan ta samu dawowa gida.

Kalli bidiyon anan:

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment