Thursday, 5 September 2019

Kasar Afrika ta kudu ta rufe ofishin jakadancinta a Najeriya

Ofishin jakadancin Kasar Afrika a Najeriya ya dakatar da aiki inda ya bayyana cewa ya tsayar da duk wata hulda da yake yi a Najeriya saboda fargabar za'a iya kaimai hari.
Jakadan Afrika ta kudun a Najeriya, Bobby Moroe ya bayyanawa manema labarai cewa sun kulle ofishin nasune saboda sun samu rahotannin cewa ana tare motoci ana fito da 'yan kasar Afrika ta kudu tare da far musu.

Dan haka sun kulle ofishin jakadancin dan gudun fargabar kai musu hari har sai lamurra sun daidaita.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment