Saturday, 7 September 2019

Kasar Afrika ta kudu tace Najeriya ta daina barin mutanenta masu aikata laifi na shiga kasarsu

Ministar hakojar kasashen Waje ta kasar Afrika Ta kudu Naledi Pandor a wani taron manema labarai da ta yi ta bukaci Najeriya data daina barin 'yan kasarta masu aikata laifukan sayar da kwaya, safarar mutane da sauran laifuka suna zuwa kasarta.

Pandor ta kara da cewa 'yan Najeriya dake zaune a kasar ta Afrika ta kudu suna aikata laifukan safarar miyagun kwayoyi da safarar mutane.

Saidai ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Geofrrey Onyeama ya caccaki ministar inda yace be kamata ta rika wadannan kalamai na tunzura mutane ba a yayin da ake tsaka da tashin hankali ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment