Wednesday, 11 September 2019

Kasar Saudiyya ta kama wani shehin malamin kasar daya soki shirin ta na Nishadi

Mahukuntan kasar Saudiyya sun kama farfesan Shari'ar musulunci kuma malami a jami'ar Qassim, Jamal Khashoggi bisa sukar shirin kawo abubuwan shakatawa kasar ta Saudiyya inda ya bayyana cewa hakan ya sabawa al'adar kasar.Aljazeera ta bayyana cewa an kama Jamal ne bayan da wani bidiyonshi yana sukar shirye-shiryen nishadin da kasar ke yi ya bayyanana.

Akwai shirye-shiryen nishadi da kasar ta Saudiyya ta shirya karkashin jagorancin yarima Muhammad bin Salman inda aka gayyato mawakan kasar Amurka irin su, 50 Cents, Mariah Carey, Sean Paul, Janet Jackson dadai sauransu, an kuma dake wa mata haramcin tuki da kuma dake haramta taron maza da mata a guri daya.

Shirye-shiryen wani salone na jawo hankalin Duniya musamman kasashen yamma wajan zuba jari a kasar, kasar Saudiyya ta fara daukar wannan matakine bayan da farshin mai ya fara yin kasa a shekarar 2014.

Kuma an kama masu rajin kare hakkin bil'ada na kasar da dama da kuma wasu shehinnan malamai da suka soki wannan shiri.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment