Tuesday, 10 September 2019

Kisan 'Yan Shi'a 3 a Kaduna: Bamu harbi koda kiyashi ba>>Inji 'Yansanda

Hukumar 'yansanda ta haramta tattakin 'yan Shi'a, Amma duk da wannan haramci tuni 'ya'yan kungiyar ta IMN suka fita yin tattakin a jihohi da dama na Najeriyar.


Kuma tuni kungiyar ta ce jami'an tsaro sun kashe mata mutum uku a Kaduna da Gombe da Katsina da Ilela ta jihar Sakkwato da kuma Bauchi a tattakin da suka fita yi na Ranar Ashura.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar wa da BBC cewa ba su harbi ko da kiyashi ba, amma sun fatattaki 'yan shi'ar mabiya IMN a lokacin da suka fito tattakin.

Kungiyar ta IMN ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Twitter mai suna @SZakzakyOffice, inda ta ce su ne na mutanen da jami'an tsaron suka harbe mata.

Ta kara da cewa an yi tattakin lafiya an watse a jihar kano ba tare da hargitsi ba kamar sauran sassa.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment