Monday, 9 September 2019

Kotu ta yi watsi da karar dake kalubalantar zaben gwamna El-Rufai na Kaduna

Kotun sauraren karar zabe dake Kaduna ta yi watsi da karar dake kalubalantar nasarar gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin zababben gwamnan jihar da dan takarar jam'iyyar PDP,Isah Ashiru Kudan ya shigar.Kotun bisa jagorantar me shari'ar Ibrahim Bako ta bayyana cewa Isa Ashiru ya kasa gabatar da kwakkwarar hujjar kalubalantar zaben gwamna El-Rufai.

Dan haka ta tabbatar da El-Rufai a matsayin zababben gwamnan jihar ta Kaduna.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment