Friday, 13 September 2019

Kuma dai: Chelsea ta sake karya dikar FIFA ta sayi dan shekaru 14

A karo na biyu an sake samun kungiyar kwallon kafa ta chelsea da shiga matsalar karya dokar FIFA na sayen dan wasan da baikai shekaru 16 ba. A yanzu dai dama Chelsea na fama da takunkumin hana sayen 'yan wasa saboda irin wannan laifi data taba aikatawa a baya amma ga dukkan alamu an sake kwatawa.Wasu labaran sirri da jaridar kasar Jamus me suna Der Spiegel ta ruwaito sun bayyana cewa Chelsea ta shiga wata yarjejeniya dan dan kwallon kasar Asutria, Thierno Ballo wanda yanzu shekaru shi 17 amma a lokacin da suka kulla yarjejeniyar yana da shekaru 14 ne a Duniya inda Chelsea ta bashi kudi, Yuro miliyan 10 lokacin yana makarantar horaswa ta Bayern Leverkusen a shekarar 2016.

Bayan kulla yarjejeniyarne sai ya koma kungiyar Viktoria Koln dan a fara shiryashi ya fara gogewa kamin ya koma Chelsea.

Hukunar kwallon kafa ta hana fara tattaunawa da dan wasan da baikai shekaru 16 ba.

Da aka tuntubi me magana da yawun Chelsea ya bayyana cewa ba zai ce komai ba akan maganganun dake yawo kan kwatirakin da aka yi a asirceba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment