Wednesday, 11 September 2019

Kungiyar kasar Amurka ta fara magana da Messi kan barinshi Barcelona

Rahotanni daga kasar Sifaniya na cewa David Beckham ya fara tuntubar tauraron dan kwallon Barcelona, Lionel Messi akan komawa kungiyarshi ta Inter Miami dake kasar Amurka.Gidan rediyon Catalunya dake kasar Sifaniyanne ya bayyana haka kamar yanda The Mirror UK ta ruwaito.

Tuni dai dama Beckham ya bayyana cewa yana da burin kawo Messi ko Ronaldo kungiyar tashi.

Ya samu karfin gwiwar neman Messi bayan da labari ya watsu cewa A kwantirakin da Messin ya sakawa Hannu na bugawa Barcelona wasa zai iya barin kungiyar duk sanda yaso.

Saidai rahotanni sun bayyana cewa, Barcelonar ta shirin baiwa Messi damar buga mata wasa har yayi ritaya.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment