Monday, 9 September 2019

Kwanaki 100 akan Mulki: Gwamnan Kano ya ciri tuta tsakanin gwamnonin Najeriya

Wata kungiyar kula da haarkar Dimokradiyya da kuma sa ido akan yanda ake gudnar da Mulki a nahiyar Afrika, ADAN dake kasar Senegal ta bayyana gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin na daya cikin gwamnonin Najeriya a kwanaki 100 da gwamnonon suka yi a akan mulki.Dan haka kungiyar ta shirya karrama gwamnan da kyauta ta musamman.

Me magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ne ya fitar da wannan sanarwa ga manema labarai ranar Lahadi inda yace kungiyar ta aikewa da gwamnan takardar yabd inda ta yaba mai musamman kan habbaka ilimin 'ya'ya mata.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment