Sunday, 8 September 2019

Kwankwaso Zai Bude Kwalejin Koyon Jinya Da Kuma Unguzoma A Jihar Kano

Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Rabi'u Musa Kwankwaso zai bude kwalejin koyon jinya da unguzoma a jihar Kano.Za a  bude kwalejin ne a garin Kwankwaso dake jihar Kanon Dabon Nijeriya.

Wannan ba karamin ci gaba bane a fannin lafiya, sai dai ya kamata Kwankwaso ya yi abunda ya dace wurin ragewa kwalejin kudi kasancewar kwalejin kudi ce ba ta Gwamnati ba.

A Nijeriya musamman a Arewa maso Yamma akwai karamcin makarantun lafiya sosai, wanda hakan babbar barazana ce ga al'ummar yankin.

Duk da cewa a Arewacin Nijeriya Kwankwaso na daya daga cikin manyan 'yan siyasa dake taimakawa 'ya'yan talakawa, amma ya kamata a yi wa wannan makaranta tsarin kudin da ko 'ya'yan talakawa za su iya shigarta.

A Arewa maso Yamma fannin lafiya musamman fannin ungozoma da kuma koyon jinya yana da wahalar samun gurbin karatu ga 'ya'yan talakawa, amma a wannan karon muna fatan Kwankwaso zai saukakewa 'ya'yan talakwa shiga cikin wannan fanni.

Babu shakka Kwankwaso ya yi kokari wurin yunkurin bude wannan makaranta, sai dai abunda ake so shine saukakewa 'ya'yan talakawa damar shiga wannan makaranta.
Rariya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment