Saturday, 7 September 2019

Liverpool na son sayen dan kwallon Najeriya

Juventus na sha'awar 'yan wasan Manchester United guda uku - David de Gea mai shekara 28 da Eric Bailly dan shekara 25 sai kuma Nemanja Matic mai shekara 31- kuma za ta mika tayi kan 'yan wasan a karshen kakar bana, a cewar rahoton Gazzetta Dello Sport.


Goal ta ruwaito Liverpool na cikin kungiyoyin da suke saka wa Samuel Chukwueze na Najeriya mai shekara 20.

Atletico Madrid ta shirya tsaf domin daukar Christian Eriksen mai shekara 27 daga Tottenham a watan Janairu mai zuwa, in ji jaridar Express.Jaridar Star kuwa ta ruwaito cewa za a sake bai wa Tottenham damar daukar Paulo Dybala na Juventus mai shekara 25, wanda aka yi wa kudi fan 65, idan an sake bude kasuwar saye da musayar 'yan wasa a Janairu mai zuwa.


Kocin Manchester City Pep Guardiola zai sake neman dan wasan baya ko da kuwa dan kasar Faransa Aymeric Laporte 25 ya kusa dawowa daga jinya, in ji rahoton jaridar Mail.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce ya ji dadi da sauyin da aka samu game da dan wasan gaba Gareth Bale kuma yi imanin cewa shi da Eden Hazard za su zama wani muhimmin bangare na nasararsa a Madrid. (ESPN)

Sai dai Bale ya ce yana "sa ran haduwa da karin kalubale" kafin a samu "matsaya" game da makomarsa a kungiyar, kamar yadda kafar Sky Sports ta ruwaito.

Dan kasar Armenia Henrikh Mkhitaryan ya ce ya bar Arsenal ne zuwa Roma saboda karancin damar wasa da yake fuskanta a Arsenal. (Mirror).
BBChausa.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment