Saturday, 14 September 2019

Liverpool ta lallasa Newcastle da ci 3-1: Kungiyar, Mane da Salah sun kama tarihi

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Newcastle United da ci 3-1 a wasan da suka buga yau na gasar cin kofin Premier League. Newcastle ce ta fara sakawa Liverpool kwallo ta hannun dan wasanta, Willems.Saidai tun kamin a tafi hutun rabin lokaci Sadio Mane ya rama mata kwallon hadi da kari inda yace kwallaye 2, bayan dawowa hutun rabin lokaci ne ana mintuna 72 da wasa Mohamed Salah ya kara ciwa Liverpool kwallo ta 3 inda a haka aka tashi wasan 3-1.

Da wannan nasara kungiyar Liverpool ta kafa tarihin kasancewa kungiyar kwallon kafa ta farko data ci wasannin ta 14 a jere sannan kuma a kowane wasa tana cin kwallaye akalla 2.

Hakanan Sadio Mane ya kafa tarihin kasancewa dan kwallon Premier League na farko da ya bugawa wata kungiya wasanni 50 a gida ba tare da an yi nasara akanshi ba. Mane ya bugawa Liverpool wasanni 50 a gida kuma a ciki yayi nasa a guda 41 an yi kunnen doki a 9, shi kadai ke da irin wannan tarihin a Premier League.

Hakanan shima Mohamed Salah ya kafa tarihin ci da kuma taimakawa a ci kwallaye 50 a kungiyar ta Liverpool a wasanni 41 da ya buga mata.

Dan wasan Liverpool din,Origi ya tafi jiyya bayan da ya samu rauni da farifarin wasan na yau.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment