Wednesday, 4 September 2019

Lukaku ya nemi a bi mai hakkin wariyar launin fata da aka nuna mai: Saidai wata kungiya tace ba wariyar launin fata aka nuna mai ba

Tauraron dan kwallon Inter Milan, Lukaku da ya koma kungiyar daga Manchester United ya nemi a bi mai hakkinshi kan zagin nuna waroyar launin fata da magoya bayan Cagliari suka mai a wasan da suka buga,Lahadin data gabata wanda ya kare Inter na cin 2-1.Inter ta samu bugun daga kai sai Gola,Kuma tun tasowarshi kamin ya buga kwallon aka fara mai ihun Biri a filin, bayan da yaci kwallon sai ihun ya karo, be yi murna ba kawai sai ya juya yana kallon magoya bayan Cagliarin.

Bayan wasan Lukaku ya nemi abi mai hakkinshi, saidai hukumar Seria A ta bayyana cewa zata iya bi mai hakkin ne kawai idan yana da kwakkwarar hujja.

Wata kungiya wadda tace tana cikin wanda suka tareshi a lokacin da ya fara zuwa Italy tace tana bashi hakuri akan abinda aka mai a Cagliari da yake tunanin kamar wariyar launin fatane.

Kungiyar tace su a Italiya suna da banbancin yanda suke goyon bayan kungiyoyin kwallo da kuma adawa ba kamar sauran kasashen Turai ba, tace wannan abu da suke yi suna yine kawai da nufin tunzura abokan hamayyarsu amma ba dan wariyar launin fata ba kuma zasu ci gaba ba zasu daina ba, suna fatan Lukakun zai fahimta.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment