Tuesday, 17 September 2019

Lukaku ya sake funkantar waruyar launin fata

Wata tashar talabijin a Italiya ta ce sam ba za ta sake aiki da wani mai yi mata sharhi kan kwallon kafa ba,bayan ya furta wasu kalaman nuna wariyar launin fata kan dan wasan gaba na Inter Milan, Romelu Lukaku.
Da yake sharhi a tashar talabijin ta TopCalcio24, Luciano Passirani ya ce : ‘’idan ka yi fito-na- fito da shi, tabbaci hakika zai kasheka. Hanya mafi sauki ta tunkararsa ita ce kawai watakila ka ba shi ayaba goma ya ci’’.

Shugaban sashen shirye – shirye na tasahr talabijin din Fabio Ravezzani ya ce duk da Passirani ya nemi afuwa na take, tashar ba za ta sake mu’ammala da shi ba a shirye – shiryen su.

‘’Passirani dai shekarunsa 80 ne, wajen jijina wa Lukaku ya yi amfani da kalaman nuna wariya,’’ in ji Ravezzani.

"ina ganin wannan sake ne, da rashin amfani da kaifin tunani, kuma ba zan lamunci haka ba,’’ ya kara da cewa.

A wannan kaka Lukaku ya koma Inter Milan ta Italiya daga Manchester United.

Kwanan nan aka nuna wa Lukaku wariya a yayin wasan Inter da Cagliari inda ya ci wa kungiyarsa kwallo daya daga bugun daga kai sai mai tsaron raga.
RFIhausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment