Friday, 6 September 2019

Mace mai shekara 73 ta haifi 'yan biyu

Wata mata mai shekara 73 a duniya da ke kudancin jihar Andhra Pradesh a kasar India ta haifi 'yan biyu mata.


Likitoci ne suka karbi haihuwar 'yan biyun wanda aka yi nasarar yi mata dashensu a mahaifarta.

Likitan matar, Dakta Umar Sankar ya fada wa sashen BBC na Telugu cewar matar da jariran suna cikin koshin lafiya.Mai jegon, Mangayamma Yaramati ta ce ita da mai gidanta, dan shekara 82 a duniya sun dade suna neman haihuwa amma kuma ba su samu ba har sai zuwa wannan lokaci.

Mai gidanta, Sitarama Rajarao, shi ma ya fada wa BBC jim kadan da haihuwar 'yan biyun cewa suna cike da farin ciki mara misaltuwa.


Sai dai kuma kwana daya tsakani, Mista Rajarao ya samu matsalar mutuwar barin jiki inda a yanzu yake samun kulawa a asibiti.

''Ba mu da ikon yin komai, duk abin da zai faru, ba makawa zai faru. Komai yana hannun Ubangiji'', a cewar Mista Rajarao lokacin da aka tambaye shi kan ko wa zai kula da jariran idan har ta Allah ta kasance akansu duba da tsufansu da yanayin shekarunsu.

Samun magada abu ne mai muhimmanci ga ma'auratan da suka ce ana nuna musu wariyar launin fata a kauyensu sakamakon tsawon lokacin da aka dauka ba tare da sun haihu ba.

Miss Yaramati ta ce sau da dama mutane kan yada mata magana kan rashin samun haihuwa.

Ta ce mun yi iya yinmu sannan kuma mun ga likitoci daban-daban amma wannan rana ita ce rana mafi farin ciki a rayuwata.

An dai haifi 'yan biyun ta hanyar yi wa mahaifiyarsu tiyatar CS, hanyar da aka fi amfani da ita a irin yanayin da mahaifiyarsu take ciki.

A shekarar 2016 ma wata mata 'yar India mai shekaru 70, Daljinder Kaur ta haifi santalelen da.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment