Saturday, 14 September 2019

Magoya bayan PSG sunwa Neymar Ihu da zagi a wasanshi na farko a kungiyar a kakar bana, yaci kayatacciyar kwallo

A wasan da kungiyar PSG ta buga da Strasbourg a yau na neman daukar kofin League 1 ta sha da kyar da ci 1-0. Neymar ne ya ci mata kwallon ta hanyar watsiya yayin da ake mintuna 91, kiris a tashi wasan.Saidai Neymar din ya sha ihun da zagi a gurin magoya bayan PSG tun daga farkon fara wasan har aka gama anna duk da wannan bai hanashi cin kwallo ba, kuma koda bayan da yaci kwallon sun ci gaba da mai wannan Ihun.

Masoyan PSG dai na mayarwa da Neymar martanine kan nunawa da yayi baya son zama a kungiyar yana son komawa tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona a yayin da aka bude kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa, saidai hakarshi bata cimma ruwa ba bayan da Barca din ta kasa biyan kudin sayenshi wanda wasu rahotanni sun bayyana cewa har kuka sai da yayi.

Bayan kammala wasan na yau Neymar ya shaidawa manema labarai cewa a bayyane yake kowa yasan abinda ya faru shi beda abinda zai cewa magoya bayan PSG kawai dai yasan idan suna goyon bayansu zasu kara musu karfin gwiwa su buga kwallo me kyau.

Ya kara da cewa idan shi an mai ihu akwai fa 'yan wasa 24 a kungiyar su ai basu cancanci a musu ihu ba. Neymar yace a shekaru 2 da suka gabata lokacin da yazo kungiyar sun mai tarba me kyau kuma ba zai taba mantawa da hakan ba.

Game da kwallon da yaci kuwa yace yana farin ciki da ita.


Kalli kayatacciyar kwallon da Neymar din yaci a kasa data baiwa PSG maki 3.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment