Tuesday, 17 September 2019

Makarantun jihar Kwara sun ki karbar litattafan karatun da Bukola Saraki ya basu

Makarantun jihar Kwara sun ki amincewa da litattafan karatun da tsohon kakakin majalisar dattijai wanda kuma tsohon gwamnan jihar ta Kwara, Bukola Saraki ya aika musu.Rahotanni daga jihar na cewa gwamnatin jihar ta bayyana cewa dalilin kin karbar takardun shine ba'a biyo hanyar daya dace wajan bayar dasu ba, kamata yayi a aika da litattafan ma'aikatar ilimi ta jihar wadda itace keda hakkin rabawa makarantun jihar kayan rubutu da karatu.

Sanarwar da Daily Trust ta ruwaito ta kara da cewa, kuma kayan karatu da za'a yi amfani dasu a makarantun jama'a da aka yi amfani da kudin gwamnati wajan samar dasu be kamata a buga hoton wani dan siyasa a jiki ba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment