Saturday, 14 September 2019

Man City ta sha kashi a hannun Norwich da ci 3-2

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sha kashi a hannun Norwich da ci 3-2 a wasan meman daukar kofin Premier League da suka buga a yau. Norwich na cin 2-1 aka je hutun rabin lokaci.


Bayan dawowa daga hutunne sai aka karawa City kwallo daya amma ana gaf da tashi suka kara kwallo daya suma, an tashi wasan 3-2.

Aguero da Rodri ne suka ciwa City kwallonta yayin da Pukki dan Cantwell da Mclean suka ciwa Norwich nata kwallayen.

Aguero ya kafa tarihin cin kwallaye a dukka wasannin farko guda biyar daya bugawa kungiyar tashi abinda babu wanda ya taba yi a gasar Premier League in banda Rooney da Marigayi Reyes na Arsenal.

Yanzu Liverpool ta baiwa City tazarar maki 5 kenan akan teburin Premier.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment