Monday, 16 September 2019

Manoman masara a Najeriya 'sun ji dadi da Buhari ya rufe iyakoki'

Kungiyar manoman masara ta Najeriya ta ce ta gamsu da yadda farashin masarar da aka noma a kasar ya yi tasiri.


A yanzu ana sayar da buhun masara kan naira 9,000 wanda a baya ana sayar da shi ne naira 5,000.

Shugaban kungiyar manoman masara a Najeriya, Bello Abubakar Annur Funtuwa, ya ce rufe iyakokin kasar da aka yi da kuma hana bayar da kudin waje da babban bankin Najeriya ya yi ga masu shigowa da abinci a cikin kasar sun taimaka wajen samar wa manoman masara farashi mai kyau.

Kungiyar manoman masarar ta ce tana son ganin ta fara fitar da masara zuwa kasashen waje nan ba da dadewa ba.Bello Funtuwa ya shaida wa BBC cewa akwai isasshiyar masarar da aka noma wacce za ta isa ciyar da 'yan kasar.

"Noman da aka yi na bara an noma a kalla tan miliyan 20, kuma yawanci kamfanonin da ke sayen masara don sarrafawa ba su saya a wajenmu ba, sai aka bar mu da ita. Yanzu haka akwai masarar da za ta isa kamfanoni su saya, masu abincin kaji ma su saya a kuma samu ta ci.

"Mu yanzu nan gaba kadan ma fatanmu shi ne bayan mun wadata kasa, sai kuma mu fara fitar da masarar nan zuwa kasashen waje," in ji Bello Funtuwa.

Sai dai kuma ya ce wannan ba zai sa su yi amfani da damar wajen tsawwala farashin masarar ba, "tun da akwai abinci wadatacce kuma ga wata nan sabuwa na zuwa, ai rashin wadatar abu ne yake sa farashinsa ya yi sama," a cewar shugaban kungiyar manoman.

Ya kara da cewa suna daukar matakai a kungiyance don hana tashin farashin masarar.

"Akwai wani kwamiti da ake kira GNP karkashin hadin gwiwar kungiyarmu da gwamnatin tarayya da sauran kamfanoni, shi ke iyakance farashin yadda za a sayar da masarar don cimma matsaya," in ji shi.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment