Saturday, 7 September 2019

Masu garkuwa da mutane sun kone wanda suka sace kurmus bayan da 'Yan uwanshi suka kasa biyan kudin fansa


Wannan bawan Allahn sunanshi Jamilu dan jihar Kadunane da masu satar mutane dan kudin fansa suka saceshi, sun bukaci a biyasu kudin fansa kamin su sakeshi kuma an kai musu, saidai saboda ba a kaimusu yawan kudin da suka yi tsammani ba sun kasheshi.

Sun kasheshine ta hanyar kona shi, kamar yanda Ibrahim Bello ya bayyana a shafinshi na Facebook sannan suka kira 'yan wanshi da su je su daukeshi.

'Yan uwan Jamilu sun ganeshine da kaya da takalminshi da suka tarar a wajan, sai kuma kokon kanshi da sauran kasusuwan jikinshi da suka yi saura.

Muna fatan Allah ya jikanshi


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment