Monday, 9 September 2019

Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 6 a hanyar Abuja-Kaduna

Da yammacin jiya, Lahadi ne masu garkuwa da mutane suka sace mutum 6 akan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Mutanen dai sun fitone daga garin Offa na jihar Kwara zuwa Kaduna.Duk da dai jami'an tsaron 'yansanda basu tabbatar da wannan lamari ba amma kungiyar 'yan Offa din ta tabbatar da satar inda tace tuni shiri yayi nisa na ganin an sake wadanda aka sace din.

An sace mutanen ne a wajajan Rijana,  kamar yanda The Nation ta ruwato.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment