Thursday, 12 September 2019

Mata a kasar Saudiyya sun fara shigar da suka ga dama a bainar Jama'a

A yayin da kasar Saudiyya bisa jagorancin yarima Muhammad Bin Salman ke samar da hanyoyin saukaka rayuwar shakatawa da walwalar rayuwa, an samu wasu mata da suka fara fita bainar Jama'a babu Abaya.
Wata me suna Mashael al-Jaloud 'yar shekaru 33 ta fita waje kai ba dan kwali kuma babu abaya a tare da ita sai wando da riga.

Ta rika yawonta haka inda ta shiga guraren taron jama'a kamar yanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito. Bayan kayan data saka, talakalmin da ta saka me kwas-kwas ya taimaka wajan jawo hankulan mutane kanya.

Wata ta matsa kusa da ita tace ke ko wata tauraruwace? Jaloud ta amsa mata da cewa ita ba tauraruwa bace, macece kamar kowace mace 'yar kasar Saudiyya.

Ta bayyana yanda ta je shiga wani shago amma jami'an dake tsaron shagon suka hana ta shiga saboda bata saka kayan mutunci ba, ta yi kokarin nuna musu bidiyon yari man kasar da yake cewa saka abayar ba dole bace amma suka hanata.

Data koma gida sai ta saka wannan lamari a shafinta na Twitter, shagon ya mayar mata da martanin cewa baya barin matan da basu sa kayan da suka rufe jikinsu ba da suka sabawa al'adar kasar shiga shagonsu.

Wannan lamari yayi kamari sosai har ta yanda wani dan gidan sarautar kasar ta Saudiyya yaga abin ya kuma yi Allah wadai da ita ya kuma bayar da umarnin hukuntata.

Jaloud dai ta hakikance akan cewa ita fa so take ta yi rayuwarta yanda take so ba tare sa ana gaya mata abinda zata yi ba, ta kara da cewa saka abayar ba addini bace, da addini ce me yasa matan kasar Saudiyyar idan suka fita wasu kasashe basu sakata?

Saidai duk da wannan kafiya ta kin saka abaya a bainar jama'a ta Jaloud dole tana sakata idan zata wajan aiki saboda a wajan aikin saka abaya dolene kuma ba'a yadda mace ta saka kaya masu shara-sahara ba idan ba haka ba kuwa za'a koreta daga aiki.

Itama wata me rajin kare hakkin bil'adama me suna, Manahel al-Otaibi -yar shekaru 25 ta bayyana cewa tuni ta yi watsi da saka abaya, watanni 4 kenan duk inda zata haka take shiga ba mayafi ko abaya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment