Sunday, 15 September 2019

Matashin da aka kama da zargin saidawa Boko Haram Doya yace yana matukar jin haushin GwamnatiMusa dan shekaru 17 da haihuwa na zama ne a arewa maso gabashin Najeriya, ya bada labari mai sosa rai. Ya ce a lokacin da yake da shekaru 8 da haihuwa, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki a kauyensu suka kona shi kurmus. Dole iyayen Musa suka koma wani wuri da zama, amma bayan shekaru biyu mayakan na Boko Haram suka sake kai hari a kauyen. Wannan karon, mayakan sai da suka yi awon gaba da duk dabbobin dake gidansu Musa. Don ya taimakawa iyayensa, Musa ya fara saida doya, amma a lokacin da yake da shekaru 13 da haihuwa, hukumomin Najeriya suka kama shi akan zargin yana saidawa ‘yan boko haram doya.Musa ya ce ba ka iya gane waye dan boko haram waye ba dan boko haram ba, don haka shi bai san wa da wa ya saidawa doya ba. Ya kwashe kusan shekara daya tsare a gidan yari.

Musa ya ba da wannan labarin ne ga wakilan kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Human Rights Watch da ake kira HRW a takaice, a lokacin da suka je Maiduguri babban birnin jihar Borno kwanan nan.

Har yanzu Musa na jin zafin abinda ya faru da shi.

Ya fadawa kungiyar ta HRW cewa, “ya na jin haushin gwamnati sosai saboda babu laifin da ya yi. Ya kara da cewa kamata yayi gwamnati ta zurfafa bincikensa kafin kawai ta tsare mutum.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment