Monday, 16 September 2019

Me Dokar Bacci..: An kori dansandan da aka kama da satar Talabijin da takalma daga aiki

Hukumar 'yansandan jihar Jigawa ta kama wani jami'inta me suna Abdullahi Yusuf da aka samu da satar talabijin da takalma.Kwamishinan 'yansandan jihar, Bala Senchi ne ya bayyawa Premium Times haka a ranar Juma'ar data gabata inda yace dansanda ya kamata ya kasance amintacce saboda ana bashi amanar mutanene dan haka an koreshi daga aiki.

Ya kara da cewa, dama an tsareshi na tsawon watanni hudu a baya saboda wata sata da yayi a baya.

Wani jami'in dan sandan daya bukaci kada a bayyana sunanshi yace sati biyu bayan sakin Yusuf bisa satar da yayi a bayane ya sake yin wannan satar.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment