Sunday, 8 September 2019

Messi na da damar barin Barcelona inji shugaban kungiyar

Shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya bayyana cewa tauraron dan kwallon kungiyar, lionel Messi nada damar barin kungiyar a kowane lokaci yake da muradin yin hakan.Ya bayyana hakane ga gidan talabijin din kungiyar a hirar da suka yi dashi.

Messi ya sakawa Barcelona hannu a kwantirakin buga wasa na shawon shelaru 4 a shekarar 2017 saidai Bartomeu ya bayyana cewa Messin nada damar barin kungiyar kamin lokacin idan yana so.

Yace damace akae baiwa manyan 'yan wasa wanda kuma kamin Messi, Xavi, Iniesta, da Puyol duk sun sami irin wadannan damarmaki amma suna da yakinin cewa Messi yqna tare dasu, zai ci gaba da buga musu wasa daga nan har zuwa karshen kwantirakinshi a shekarar 2021 dama gaba da haka.

Tun shekarar 2001 Messi ke bugawa Barcelona kwallo.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment