Saturday, 7 September 2019

Messi yafi Mohamed Salah>>Inji Wenger

Tsohon me horas da kungiyar Arsenal,Arsene, Wenger yayi magana akan fushinda Sadio Mane na Liverpool yayi da abokin wasanshi, Mohamed Salah kan kin bashi kwallo da yayi ya ci a wasan da suka buga da Burnley da suka tashi 3-0.
Da yake hira da beIN sport, Wenger ya bayyana cewa, Salah dan kwallo ne me kyau dake da kokarin kaiwa matakin Messi amma shi Salah a koda yaushe burinshi shine yaga ya ci kwallo da kanshi, yana da sonkai.

Saidai duk da yana so yaci kwallo, Messi yakan duba yanayi yaga inda ya kamata yaci da kanshi da inda kuma ya kamata ya baiwa wani yaci.

Wenger ya kara da cewa, yana son Salah kuma shima watakila nan gaba ya canja salon kwallon tashi.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment