Saturday, 14 September 2019

Mikiya ta kashe wani yaro a Somaliya

Iyalai a yankin Habasha na kasar Somaliya sun ce suna fama da hare-haren da mikoyoyi ke kai musu.


A kalla yaro daya ne ya mutu sannan wasu biyun suka ji rauni a gundumar Gaashaamo.

Muno Shuayb ita ce mahaifiyar daya daga cikin yaran da suka ji raunin.Ta shaida wa BBC cewa tana cikin dakinta a lokacin da ta ji ihun dan nata.

"Sai muka fito da gudu daga cikin gida. Na ga mikiyar na rike da dana tana cizonsa. Yana ta ihun kiran Mama...Mama! Sai na yi maza na dauki sanda na kori mikiyar."

Wani babban jami'in dan sanda Mohamed Hassan, ya ce an tsaurara tsaro a yankin. An kuma ba su umarnin harbe mikiyoyin a duk sanda suka kawo hari.

"A yanzu haka 'yan sanda na samame a wajen. An kai 'yan sanda da dama inda suka zagaye dajin.

"Mun ba su umarni su harbe mikiyar, amma har yanzu ana nemanta."

BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment