Tuesday, 10 September 2019

Muna da hujjar cewa Kotu zata sauke Buhari>>Atiku

Jam'iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa a babban zaben daya gabata, Alhaji Atiku Abubakar ta jawo hankalin kotun sauraren kararakin zaben shugaban kasa data bayyana Atikun a matsayin wanda ya yayi nasara.PDP da Atiku sun ce ya kamata kotun tasan cewa Buhari kwata-kwata be kamata ma ace yayi takarar shugaban kasar ba saboda be cancanci yin hakan ba.

Daya daga cikin lauyoyin Atikun, Mike Ozekhome ya bayyana cewa Atiku ya gabatarwa da kotu Shaidu masu karfi dake nuna cewa shine yaci zabe amma aka kwace mai dan haka suke kira ga kotun a matsayin ta na guri na karshe da marasa karfi ke zuwa dan a kwatar musu hakkinsu ta yi adalci a wannan shari'a.

Yace yanzu dai 'yan Najeriya sun zurawa kotun ido suna jiran jin yanda zata kaya.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment