Wednesday, 18 September 2019

Muna kokarin Bunkasa tattalin Arzikin Najeriya ta yanda zai rika habaka cikin sauri kamar na kasar China>>Ministar Kudi

Ministar kudi, Zainab Ahmad ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya iya kokarinta wajan ganin tattalin arzikin Najeriya na habaka cikin sauri irin na kasar China da sauran kasashen Duniya.
Zainab ta bayyana hakane a wajan taron ganawa da manema labarai ranar Litinin inda take magana akan taron tattalin arzikin Najeriya da za'a yi nan gaba, tace gwamnati na kokarin ganin Najeriya ta shiga sahun kasashe 100 na Duniya da aka fi samun saukin yin kasuwanci a cikinsu.

Ta kara da cewa akwai tsarin hadun kai da masana'antu masu zmaan kansu da gwamnati ta fito dashi da zai yi aiki a sassan kasarnan wanda irin na kasar Chinane da sauran kasashen Duniya dan bukasa kasuwanci.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment