Wednesday, 18 September 2019

'Na gamsu da shirin Buhari kan tattalin arziki'>>Sarkin Kano

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana cewar kasashen da ke mokobtaka da Najeriya ba sa taimaka mata wajen kare tattalin arzikinta.


Sarkin na Kano Muhammadu Buhari ya bayyana wa BBC cewar dole ce ta sa Najeriya ta dauki matakin rufe dukkan iyakokinta, domin ta bunkasa tattalin arzikinta musamman abin da ya jibanci noman shinkafa.

Hakan ne ya sa Sarkin yaba wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari kan matakin rufe iyakokin kasar daga shigar da abubuwan da ake iya samarwa a cikinta.

A baya dai Sarki Sanusi ya sha sukar gwamnatin Shugaba Buhari bisa gazawa ta fannin tattalin arziki.
BBChausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment