Friday, 6 September 2019

Najeriya ba zata dauki tsauraran matakan yanke huldar Diplomasiyya da kasar Afrika ta kudu ba>>Gwamnatin Tarayya

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa, Najeriya ba zata dauki tsauraran matakai na yanke harkar diplomasiyya da kasar afrika ta kudu ba.Ministan ya bayyana hakane bayan ganawar da yayi da kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majalissar Dattijai inda yace sun tattauna yanda za'a samu mafita ta dindindin ne kan hare-haren da ake kaiwa 'yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu na kyamar baki.

Onyeama ya bayyana cewa, Najeriya ba zata yanke huldar diplomasiyya da kasar Afrika ta kudu ba saboda bayanai daga ofishin jakadancin Najeriya dake kasar sun tabbatar da cewa akawai 'yan Najeriya mazauna kasar bisa ka'ida da suka kai 800,000 dan haka daukar matakin yanke huldar diplomasiyya bazai wa Najeriya dadi ba.

Yace kuma a wannan riki sun tabbatar da cewa babu dan Najeriya ko guda daya da aka kashe saidai asarar Dukiya dan haka zasu nemi a biya wanda suka yi asarar Dukiyar diyya sannan da daukar wasu matakai na daban bana yanke huldar diplomasiyya ba.

 Yace daya daga cikin matakan da aka dauka shine wanda shugaba Buhari tayi na aikewa da wakilinshi kasar ta Afrika ta kudu dan tattaunawa da hukumomin kasar kan wannan lamari.

Yace sai bayan wakilin ya dawo ne, da rahoton da ya bayar za'a yi amfani wajan daukar mataki na gaba.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment