Saturday, 14 September 2019

Pogba, Martial, Shaw, Dalot ba za su buga wasan Leicester ba

Ole Gunnar Solskjaer na tsaka mai wuya yayin da Manchester United ke karbar bakuncin Leicester City a Old Trafford ranar Asabar.


Paul Pogba da Anthony Martial da Luke Shaw za su kalli wasan na karfe 3:00 agogon Najeriya daga wajen fili bisa dalilan jinya.

A gefe guda kuma babu tabbas a kan koshin lafiyar Aaron Wan-Bissaka da Jesse Lingard.

Yayin da Diogo Dalot da Eric Bailly su ma ke jinya, Solskjaer zai gamu da babban cikas musamman ganin yadda Leicester City ke wasa a kakar bana.Har yanzu ba a ci zakarun Premier na 2015-216 ba a bana, inda suka yi canjaras biyu kuma suka ci wasa biyu.

Ita kuwa United wasa daya kawai ta ci, inda aka ci ta daya kuma ta yi canjaras a wasa biyu.

Idan har Wan-Bissaka bai buga wasan ba to babu mamaki Ashley Young ya maye gurbinsa a bangaren lamba 2, shi kuma Marcos Rojo ya buga 3.

A cikin wadanda suke a hannu, Solskjaer zai yi bakin kokarinsa wurin karfafa 'yan wasan gabansa wadanda har yanu ake ganin kansu bai daidaita ba.

Daniel James ne yakan buga bangaren hagu a gaban kuma mai yiwuwa a fara da shi a goben, yayin da Rashford zai buga 9 saboda rashin Martial.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment