Tuesday, 10 September 2019

Ranar Ashura: Mabiya Zakzaky kadai aka hana zanga-zanga

Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta ce ba dukkan Musulmai ta haramta wa yin tattakin Ranar Ashura ba, sai 'ya'yan kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) wato magoya bayan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.


"Biyo bayan neman karin bayani da mutane ke yi kan haramta kungiyar IMN, ya zama wajibi a sani cewa haramcin yin tattakin ya shafi 'ya'yan kungiyar IMN din ne kawai.

"Saboda haka sauran al'ummar Musulmi da suke da sha'awar yin tattakin Ashura a fadin Najeriya za su iya bin sahun sauran Musulmin duniya domin yin haka."Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment