Saturday, 14 September 2019

Rashford ya ceci Man United a Old Trafford

Marcus Rashford ne ya ci bugun finaretin da ya bai wa Manchester United nasararta ta biyu a Premier ta bana kan Leicester City a Old Trafford.


Caglar Soyuncu ne ya kayar da dan wasan tawagar Ingilan a cikin yadi na 18 na Leicester a minti na 7, shi kuma lafari Martin Atkinson ya busa finareti.

Rashford ya kora Kasper Scmeichel bangaren dama, inda kwallon ta yi hagu.

Saura kiris ya kara ta biyu a cikin mintuna 10 na karshen wasan amma bugun tazarar da ya buga ya yi saman turke.

Sakamakon haka yanzu United ta koma ta 4 a teburi, yayin da Leicester ta fado zuwa ta 5.

Harry Maguire yayi kokari sosai a wasan inda taimakon da ya bayar ya hana wata kwallo da Leicester suka so ci ana gab da za'a tashi wasa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment