Saturday, 14 September 2019

Real Madrid ta sha da kyar a hannun Levente da ci 3-2

Real madrid ta sha da kyar a hannun Levente a wasan mako na 4 na LaLigar Sifaniya.


Madrid ta ci kwallo uku rigis tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a filin wasa na Santiago Bernabeu, kafin daga bisani Levente ta farke biyu, inda aka tashi wasa 3-2.

Kareem Benzema ne ya fara cilla kwallo a raga a minti na 25 tare da taimakon Daniel Carvajal.

Minti uku bayan haka Benzema ya kara ta biyu tare da taimakon James Rodriguez. A minti na 40 kuma sai Casamero ya kara ta uku ta hannun Vinicius Junior.
Minti hudu kacal da dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma tsohon dan wasan gaban Madrid din Borja Mayoral ya zare daya tare da taimakon Carlos Clerc.

Gonzalo Melero ne ya farke ta biyun bayan Jose Campana ya bugo bugun kwana a minti na 75, inda ya matsa cikin yadi na 6 kuma ya naniki Courtois tare da goga wa kwallon kansa, inda ta gangara cikin raga ba tare da wata-wata ba.

A ranar Laraba tawagar Zinedine Zidane za ta yi tattaki zuwa birnin Paris domin karawa da PSG a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Wannan nasara za ta ba su kwarin gwiwar buga wannan wasa ba tare da wata damuwa ba, musamman ganin yadda tauraron dan wasa Hazard ya dawo taka-leda.

Sai dai babu tabbas ko Luka Modric zai buga gumurzun ko kuma zai kalli wasan ne daga benci saboda raunin da ya yi a kafarsa ta hagu.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment