Tuesday, 10 September 2019

Ronaldo na daukar albashin daya kusan ninka na kowane dan wasa sau 3

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya zama na daya wajan karbar albashi mafi tsoka a gasar Seria A, bama wannan kadai ba, albashin nashi ya nunka kusan sau uku na kowane dan wasan gasar.
Gazzetta Dello ta ruwaito cewa Ronaldo na daukar albashin dala miliyan 34 duk shekara, me biye mai a matsayin na biyu shine, Matthijs de Ligt dake daukar albashin dala miliyan 8.8 da ihisanin Yuro miliyan 4 duk shekara.

Sau kuma Romelu Lukaku da ya zama na 3 da albashin dala miliyan 8.3 da ihisanin Yuro miliyan 1.5 duk shekara
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment