Wednesday, 18 September 2019

Ronaldo ya bayyana yanda shi da abokinshi suka rika zuwa barar Abinci lokacin suna yara

Tauraron dan kwallon kafar kaar Portugal me bugawa Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya bayyana yanda lokacin suna yara shi da wani abokinshi idan yunwa ta kamasu auke zuwa rokon sauran abinci a wani shagon saida abinci shi da abokinshi.

Ronaldo ya bayyana hakane a wata hira da yayi da shahararren dan jarida, Piers Morgan inda ya bayyana cewa lokacin suna yara ba zai taba mantawa ba idan sun ji yunwa shi da wani abokinshi sulan je wani shagon Mcdonalds dake kusa dasu suna tambayar ko akwai sauran Burger a basu.

Yace akwai wata mata a lokacin me suna Edna da wasu mata da suke aiki a shagon sukan basu suci, yace ba zai taba mantawa abinda auka mai ba, yace ya koma shagon aka ce mai an kulle shi yace yana amfani da wannan damar wajan watsawa Duniya cewa idan akwai wanda yasan inda wadannan matan suke yana son haduwa da su dan ya kyautata musu.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment