Wednesday, 11 September 2019

Ronaldo ya ci kwallaye 4 a wasan da Portugal da Lithuania suka buga: Ya kafa muhimman tarihi

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya ciwa kasarshi kwallaye 4 a wasan da suka buga da kasar Lithuania na neman buga gasar Euro 2020.
Ronaldo ya fara da cin kwallon bugun daga kai sai gola inda ya kara guda uku ringis daga baya, sai kuma kwallon Carvalho da ya ci kusa da za'a tashi, an tashi wasan 5-1.

Wannan ya kawo Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallaye 3 a wasa daya sau 54 kenan a tarihin kwallonshi sannan kuma ya ci kwallaye 4 a wasa daya sau 10 kenan a tarihinshi, Ronaldo ya kuma kafa tarihin kasancewa dan kwallon na farko a Duniya daya ci kasashe 40 kwallaye.

Yawan kwallayen da Ronaldo ya ciwa kasarshi ta Portugal a yanzu sun kai 93, a gaba dayan turai babu dan kwallon da ya taba ciwa kasarshi yawan wadannan kwallaye kuma hakan na nufin ya kama hanyar kamo dan kwallon kasar Iran Ali Daei wanda a yanzu shine ke rike da kambun dan kwallon da ya fi kowane dan kwallo ciwa kasarshi kwallaye da yawa inda ya ciwa kasarshi ta Iran kwallaye 109, kwallaye 17 Ronaldo ke nema ya kamo Ali.

Hakanan Ronaldo ya buge Robbie Keane inda ya zama dan kwallon da yafi cin kwallaye da yawa a wasannin neman buga gasar Euro da kwallaye 24, a baya Keane ne ke rike da wannan kambu da kwallaye 23.

Idam dai ana maganar waye gwani a bangaren kungiya to za'a ci gaba da kwatanta Ronaldo da Messi amma ifan aka zo maganar kasa ko kusa Ronaldo ya wa Messi fintinkau.

Da ake hira dashi bayan kammala wasan inda aka tambayeshi game da lashe kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d'Or, Ronaldo ya bayyana cewa, yasha fadin cewa cin kyautuka na mutum daya basu sune a gabanshi ba.

Abune da ake samu ta hanyar aiki a kungiyance amma abune me kyau, injishi.

Da aka tambayi dan shekaru 34 wanda har yanzu shekarunshi basusa ya fara nuna gajiyawa ba yaushe zai daina kwallo, yace yana jin dadin yanda yake ganin kasarshi na samun ci gaba a yanzu kuma har yanzu yana da sauran kuzari

Wannan hoton na kasa ya dauki hankula sosai musamman a shafukan sada zumunta inda aka ga wani dan kasar ta Lithuania ya durkusa yana gaishe da Ronaldon.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment