Saturday, 7 September 2019

Rufe Boda Ba Zai Bunkasa Harkar Noma Ba, Shawarar Kwankwaso Ga Shugaba Buhari

Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Injiniya Dr Rabi'u Musa Kwankwaso ya shawarci shugaba Buhari cewa rufe bodojin Nijeriya ba zai bunkasa harkar noma ba, dawo da tallafin taki da gwamnati ta janye shine kadai zai iya bawa manoma damar bunkasa harkokin nomansu.


Kwankwaso ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin taki da ta cire tare da tallawa manona dake lungu da sako na cikin kasar nan da taki taga aiki da cikawa.

Yace manoma ba sa iya sayen taki cikin saukin farashi ta yaya za ai su iya wadata abunda za su shuka da takin duba da irin kuncin rayuwar da al'ummar kasa suke ciki?

Yace yadda ake cewa an tara makudan kudade a kasar nan to in haka ne Nijeriya ta kai matsayin da za ta rabawa manomanta taki kyauta ba wai ma su saya ba.

Yace kamar yadda 'yan Nijeriya suka cancanci a basu ilmi kyauta, to haka manoman Nijeriya suka cancanci a ba su taki kyauta.

Yace rufe boda ba zai bunkasa harkar noma ba saidai ma ya kara kawo talaucin da zai sa a kasa samun kudin da za a sayo takin.

Yace yana shawartar gwamnati da ta bude boda kuma ta tallafawa manoma da wadataccen taki domin sun cancanci ayi musu hakan.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment