Friday, 13 September 2019

Rufe Iyakar Najeriya: Wasu Kaya Sun Yi Tsada, Wasu Sun Yi Arha

Rahotanni sun nuna cewa farashin wasu kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi a Najeriya sakamakon rufe iyakokin kasar da aka yi.


An rufe iyakokin ne domin hana fasa kauri musamman na shinkafa da zummar farfado da tattalin arziki da kuma inganta tsaro a Najeriya.

Muhammad Kabir Suleiman shi ne sakataren farko na kasuwar Yan Lemu wato “Orange Market” da ke Mararraba na jihar Nasarawa, ya ce ana sayar da kayan miya da sauran kayan lambu kan farashi mai sauki saidai farashin shinkafa ya tashi a makonni uku da suka gabata.

Muhammad Sani Bello mai sayar da kayan abinci ne a kasuwar ya kuma tabbatar wa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa farashin shinkafar gida ya tashi kuma ya dora alhakin akan kamfanonin da ke sarrafa ta.

Itama Lantana da ke sana'ar abincin sayarwa ta fadi yadda tashin farashin kayan abinci musamman shinkafa ya taba sana'arta wajen rage hannu akan yadda take saka abincin.

Sai dai wasu magidantan basa ganin tasirin tashin farashin kayan kamar yadda masu saida kayan abincin su ka ambata.

Yawancin 'yan Najeriya ba su tsallake ma'aunin talauci na samun dala daya a wuni, wato Naira 356, ba.
VOAhausa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment